An nada sabon Firayim minista a Nijar

Sabon shugaban kasar Nijar, Alhaji Mahamadou Issoufou
Image caption Sabon shugaban kasar Nijar, Alhaji Mahamadou Issoufou

A Jumhuriyar Nijar, sabon shugaban kasar, Alhaji Mahamadu Isufu, ya nada shugaban gwamnatinsa, wato Firayim minista.

Wanda ya samu wannan mukami kuwa, shi ne Alhaji Birji Rafini, wanda wani gogaggen dan siyasa ne.

Mukaman da ya rike a baya dai sun hada da minista da dan majalisar dokoki na kasa da kuma magajin garin Iferouane na jihar Agadez.

Nadin sabon Pira ministan dai ya biyo bayan bikin rantsar da shugaban kasar ne da aka yi dazu da rana a birnin Yamai.

A cikin jawabin da ya yi a wajen bikin, shugaba Mamahadu Isufu ya yi alkawarin yaki da tallauci da kuma karancin abinci. Sannan ya ce zai da hada kan 'yan kasar ta Nijar da kuma kare iyakokin kasar.