Bankole, Iyabo Obasanjo sun sha kaye

Bankole, Iyabo Obasanjo sun sha kayi
Image caption Alamu na nuna cewa PDP na fuskantar matsala

Sakamakon zaben 'yan Majalisar dokokin Najeriya da aka fara bayyanawa ya nuna cewa kakakin majalisar Dokoki ta Tarayya Dimeji Bankole da Sanata Iyabo Obasanjo Bello sun sha kayi.

Duka Bankole da Iyabo wacce diyar tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ce, sun sha kayi ne a hannun jam'iyyar ACN a jihar Ogun.

Wakilin BBC Umar Shehu Elleman a Lagos, ya ce Mrs. Oluremi Tinibu uwar gidan tsohon gwamnan jihar Lagos na daga cikin wadanda suka lashe zabe a jihar.

Jam'iyyar ta ACN, ta kuma lashe kujerun Majalisar Dattawa a jihar Osun, inda ta kada tsohon gwamnan jihar Oyinlola da kuma Sanata Omisore dukkansu na jam'iyyar PDP.

Ita ma dai jam'iyyar PDPn ta samu nasara a wasu jihohin, inda a jihar Kwara aka bayyana gwamnan jihar Bukola Saraki a matsayin wanda ya lashe kujerar majalisar Dattawa ta Tsakiyar Kwara.

Shi ma gwamna Danjuma Goje na Gombe, ya samu nasarar lashe kujerar majalisar Dattawa ta tsakiyar Gombe.

A Arewa maso Yamma kuwa, a jihar Kano, jam'iyyar PDP da ANPP duka sun samu nasarori a wasu mazabun jihar da aka bayyana kawo yanzu.

A jihar katsina ma, rahotanni na nuna cewa jam'iyyar CPC tana gaban jam'iyyar PDP mai mulkin jihar.