An ceto gwamnatin Amurka daga tsayawa

Kakakin Majalisar Wakilan Amurka, John Boehner Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kakakin Majalisar Wakilan Amurka, John Boehner

Batun da ya fi daukar hankali a birnin Washington shi ne cewa mai yiwuwa gwamnatin Amurka za ta tsaya cak.

To amma ga alamu, a halin yanzu, tattaunawa tsakanin 'yan siyasar kasar ta kawar da yiwuwar faruwar hakan, domin kuwa ’yan Majalisar Dokoki sun samu nasarar kubutar da ayyukan gwamnatin daga durkushewa ta hanyar cimma wata yarjejeniya a kan kasafin kudin kasar.

Batun da ya jawo takaddamar dai shi ne yawan abin da za a rage daga cikin kudaden da gwamnatin tarayya ke kashewa.

'Yan jam'iyyar Republican dai na so ne a rage dala biliyan sittin a kasafin kudin gwamnatin, yayin da su kuma 'yan jam'iyyar Democrat ke hankoron ganin an rage kasa da haka.

Daga karshe dai bangarorin biyu sun amince a rage kasafin kudin da dala biliyan arba'in.

Wannan yarjejeniya—wadda ta biyo bayan sa'o'i da ma kwanaki na tattaunawa babu kakkautawa—za ta samar da kudaden tafiyar da ayyukan gwamnati har zuwa ranar Alhamis mai zuwa, tana kuma da karin tanadi don samarwa gwamnatin kudaden kashewa har zuwa watan Satumba.

Da ayyukan gwamnati sun tsaya cak dai, da ma'aikata dubu dari takwas da ma sojojin kasar ta Amurka sun rasa albashinsu; da kuma an dakatar da duk wasu ayyukan da ba na farilla ba ne.