Za a takaita wa'adin shugabannin Cuba

Shugaba Raúl Castro na Cuba Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Raúl Castro na Cuba

Shugaba Raúl Castro na Cuba ya shammaci mahalarta babban taron Jam'iyyar Kwaminisanci ta kasar na farko a cikin shekaru goma sha hudu.

An dai kira babban taron ne don tattauna batun sauye-sauyen tattalin arziki, kuma batutuwan siyasa ba sa cikin abubuwan da za a tattauna.

Amma a jawabinsa na bude taron, Shugaba Castro ya shaidawa mahalarta cewa za a kayyade wa’adin masu rike da mukamai a kasar.

Yayan Shugaba Raúl Castro dai, wato Fidel Castro, ya mulki kasar ta Cuba—mai bin tsarin jam'iyya daya tilo—har tsawon kusan shekaru hamsin kafin rashin lafiya ya tilasta masa ajiye aikin.

A jawabin nasa, Shugaba Castro ya ce ana bukatar sababbin jini a kan mukaman shugabncin Jam'iyyar Kwaminisancin.

“Ba tare da kebance shugaban Majalisar Ministoci ko Sakataren Kwamitin Tsakiya wadanda za a zaba a wajen wannan taro ba, mun yanke shawarar takaita wa'adin masu rike da muhimman mukaman siyasa da na gwamnati zuwa shekaru biyar-biyar har sau biyu”, in ji Mista Castro.

Shugaban na Cuba ya kuma ce kuskure ne mutane su yi tunanin cewa mambobin Jam'iyyar Kwaminisanci ne kawai za su iya shugabanci a kasar:

“Wajibi ne a kawar da al'adar nan wadda gurbataccen tunani ya haifar cewa sai wadanda suka kasance matasan Jam'iyyar Kwaminisanci ne kadai za su iya rike mukaman hukuma”.

Makasudin wannan taro dai shi ne tattauna batutuwan da suka shafi tattalin arziki; ana kuma sa ran taron zai amince da wargaza tsarin tattalin arziki irin na Tarayyar Soviet da kuma baiwa kananan 'yan kasuwa dama su habaka.

Sai dai hakan zai kawo karshen rangwamen farashi ya kuma yi sanadiyyar sallamar mutane da dama a ma'aikatun gwamnati.