Gwamnatin Masar za ta kori gwamnonin kasar

Masu zanga-zanga a Dandalin Tahrir Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Masu zanga-zanga a Dandalin Tahrir

Gwamnatin rikon kwaryar Masar ta bayyana shirinta na sauke gwamnonin lardunan kasar wadanda tsohon shugaba Hosni Mubarak ya nada.

Zaman doya da manja dai na ci gaba da karuwa tsakanin sojojin kasar da kuma masu neman sauyi tun bayan tumbuke gwamnatin Mubarak a watan Fabrairu.

Yanzu dai bisa ga dukkan alamu ana tunkarar wani muhimmin mataki a sauyin da ake samu a kasar ta Masar.

Ko a ranar Juma'ar da ta gabata ma an yi babbar zanga-zanga wadda aka jima ba a ga irinta ba a Dandalin Tahrir da ke birnin Alkhira.

Karin bayani