Za a sanya ido a kan tattalin arzikin kasashe

Taron ministocin kudi na kasashen G20 Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Taron ministocin kudi na kasashen G20

Jami'an gwamnati masu kula da harkokin kudi daga kasashen duniya ashirin masu arzikin masana'antu, wato G20, sun amince da wani shiri na sanya ido sosai a kan kasashen da manufofin tattalin arzikinsu ka iya jefa duniya cikin matsalar tattalin arziki.

Ministocin kudi da jami'an manyan bankunan kasashen masu karfin tattalin arziki sun cimma wata yarjejeniya a kan hanyoyin da ya kamata a bi don tantance kasashen da ya kamata Asusun Bayar da Lamuni na Duniya, IMF, ya sanya wa ido sosai.

Burin wannan yarjejeniya dai shi ne rage yawan matsalolin da ke jefa tattalin arzikin duniya cikin hadari.

Bisa ga dukkan alamu, kasashen da ake bi dimbin bashi ko kuma yawan kayayyakin da suke fitar wa waje ya haura na wadanda suke shigowa da su za su fuskanci binciken kwakwa.

Asusun na IMF dai zai sanya ido ne sosai a kan yadda manufofin kudi na daidaikun kasashe kan shafi tattalin arzikin duniya.