Kai kayayyakin agaji Ivory Coast

'Yan kasar Ivory Coast da suke tsere Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan kasar Ivory Coast da suke tsere

Kungiyoyin agaji da ke aiki a Ivory Coast sun yi gargadin cewa jama'a na iya shiga cikin wani mawuyacin hali, musamman a birnin Abidjan, a saboda ci gaba da tashin hankalin da ake, wanda ke hana kungiyoyin damar kaiwa ga mabukata.

Majalisar dinkin duniya ta yi kira kan a bude duk wadansu kofofin taimakawa bil adama, domin samun damar kaiwa ga al'ummar da suka arto a sanadiyar fadan da ake yi a tsakanin magoya bayan Alassane Outtara wanda duniya ta amince dashi a matsayin shugaban kasar, da kuma abokin hamayyarsa Laurent Gbagbo, wanda ya ki sauka daga mulki.

Wakilin BBC yace kungiyoyin agaji basa samun damar zuwa mafi yawan wurare a birnin Abidjan a saboda lamari irin na soji. Idan kuma har aka basu damar shiga, to tabbas akwai jan aiki a gabansu.