Jam'iyyar Mista Gbagbo ta nemi a sasanta

Sojoji masu biyayya ga Alassane Ouattara Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sojoji masu biyayya ga Alassane Ouattara

Kusan mako guda tun bayan kama tsohon shugaban kasar Ivory Coast, Laurent Gbagbo, jam'iyyarsa ta yi kira a kawo karshen tashe-tashen hankula.

Shugaban jam'iyyar, wato Ivorian Popular Front, Pascal Affi N'Guessan ne ya karanta takardar da ta yi kiran sasantawa a tsakanin al'ummar kasar ta Ivory Coast.

A cewarsa, wajibi ne a maido da zaman lafiya a kuma kawo karshen daukar fansa da kwasar ganima.

Duk da samun nasarar kame birnin Abidjan da sojojin Alassane Ouattara suka yi a makon da ya gabata da kuma mika wuyan da akasarin shugabannin sojoji da 'yan sandan Mista Gbagbo suka yi, an ci gaba da fafatawa tsakanin dakarun bangarorin biyu har jiya Asabar a unguwar Yopougon, inda magoya bayan Mista Gbagbo ke da rinjaye.

Shi dai Mista Affi N'Guessan tsohon Firayim Minista ne a gwamnatin Mista Gbagbo, ana kuma yi masa kallon daya daga cikin masu tsattsauran ra'ayi a gwamnatin; don haka ake ganin wannan kira nasa a matsayin amincewa da shan kaye.

Kiran dai ya zo ne a daidai lokacin da ake sakin fursonin da gwamnatin Mista Ouattara ke rike da su a karshen mako—akasarinsu kuma ma'aikata ne da iyalan Mista Gbagbon wadanda aka kama lokacin da aka farwa fadar shugaban kasar.