Kotu ta tsare James Ibori a birnin London

James Ibori
Image caption Tsohon gwamnan Jihar Delta, James Ibori

An tsare daya daga cikin fitattun 'yan siyasar Najeriya, James Ibori, bayan ya bayyana a gaban wata kotun birnin London bisa tuhumar aikata laifuffukan da suka hada da halalta dukiyar haram da kuma sama da fadi da zamba cikin aminci.

Shi dai James Ibori tsohon gwamna ne a Jihar Delta mai arzikin mai kuma kusa a jam'iyyar PDP mai mulkin Najeriya.

Ranar Juma'ar da ta gabata ne dai aka tasa keyar tsohon gwamnan daga Dubai zuwa Burtaniya.

James Ibori dai ya musanta dukkan zarge-zargen da ake yi masa.