Firayim Ministan Japan ya godewa duniya

Firayim Ministan Japan, Naoto Kan Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Firayim Ministan Japan, Naoto Kan

Firayim Ministan Japan, Naoto Kan, ya fitar da wata sanarwa ta kusan dukkan manyan jaridun duniya, yana mai godiya ga kasahen duniya saboda yadda suka nuna alhini dangane da girgizar kasa da kuma guguwar Tsunami da suka aukawa Japan din wata guda da ya gabata.

Firayim Ministan na Japan ya kuma ce tallafin da kasashen duniya suka yi wa Japan ya karfafa al'ummarta a lokacin da suke fuskantar wani mawuyacin hali.

A yau ne kuma ake yin wasu 'yan bukukuwa a fadin kasar ta Japan domin jimami.

Al’amarin dai da ya kai ga hallaka mutane dubu ashirin da takwas, ya kuma raba mutane dubu dari da hamsin da gidajen su.