Gaddafi ya karbi shirin zaman lafiya na AU

Shugaba Gaddafi tare da tawagar AU Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Gaddafi tare da tawagar AU

Wata tawagar kungiyar Tarayyar Afirka—wato AU—wadda ke ziyara a Tripoli, babban birnin kasar Libya, ta ce Shugaba Gaddafi ya amince da shirinta na samar da zaman lafiya.

Tawagar dai, wadda ta kunshi Shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudu, da wadansu shugabannin kasashen Afirka uku, ta gana da Kanar Gaddafi jiya Lahadi, ana kuma sa ran yau Litinin za ta gabatar da shirin zaman lafiyar ga shugabannin 'yan tawaye a Benghazi.

Manyan ginshikan shirin samar da zaman lafiyar dai su ne tsagaita bude wuta nan take; da hadin kan hukumomin kasar ta Libya don samar da kayan agaji a inda ake bukata; da bayar da kariya ga 'yan kasashen waje wadanda ke Libya, ciki har da ma'aikata 'yan kasashen Afirka; da kuma tattaunawa a tsakanin bangarorin da ke yaki da nufin aiwatar da sauye-sauyen siyasar da ake bukata don magance rikicin.

Kwamishinan Tarayyar Afirka mai kula da al'amuran kiyaye zaman lafiya da tsaro, Ramtane Lamamra, ya shaidawa manema labarai cewa Kanar Gaddafi ya amince da tsagaita bude wuta a karkashin kulawar masu sa ido na kasa-da-kasa.

Mista Lamamra ya kuma ce a tattaunawar ta Tripoli an tabo batun makomar Kanar Gaddafi amma, a cewarsa, tattaunawar ta sirri ce don haka ba zai yi karin bayani a kai ba.

“Ba shakka shugabannin sun tattauna a tskaninsu a kan batun [makomar Kanar Gaddafi]; amma ba zan iya cewa komai a kan abin da suka tattauna ba saboda ban halarci zaman ba, sannan kuma tattaunawar ta sirri ce”, in ji Mista Lamamra.

Sai dai wani wakilin 'yan tawayen na Libya a Burtaniya ya shaidawa BBC cewa ba za su amince da duk wani shirin zaman lafiya da zai sa Kanar Gadafi da 'ya'yansa su ci gaba da rike madafun iko ba.

Karin bayani