Bincike ya wanke Janar McChrystal daga laifi

Janar Stanley McChrystal
Image caption Janar Stanley McChrystal

Wani binciken da Ma'aikatar Tsaron Amurka, wato Pentagon, ta yi dangane da hirar da ta kai ga tube kwamandan dakarun Amurka a Afghanistan daga kan mukaminsa ya wanke Janar Stanley McChrystal daga zargin aikata laifi.

An dai tube Janar McChrystal ne daga kan mukaminsa saboda wata hira da ya yi da mujallar nan mai suna RollingStone, inda aka yi zargin ya yi kalaman suka ga Shugaba Barack Obama da kuma mataimakinsa Joe Biden.

A lokacin da al’amarin ya faru dai Shugaba Obama ya ce Janar McChrystal ya saba ka’idar aiki a matsayinsa na kwamandan sojojin Amurka.

Sai dai binciken na Pentagon ya ce babu wata shaidar da ta nuna cewa Janar McChrystal ya saba ka’idojin Ma’aikatar Tsaron kasar ta Amurka.