Sojojin Libya na fakewa a masallatai -NATO

Laftanar Janar Charles Bouchard Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Laftanar Janar Charles Bouchard

Jagoran dakarun Kungiyar Tsaro ta NATO a Libya ya zargi sojojin da ke biyayya ga Kanar Gaddafi da fakewa a asibitoci da kuma harbin fararen hula daga rufin masallatai a birnin Misrata, wanda ke hannun 'yan tawaye.

Laftanar Janar Charles Bouchard ya ce abin da dakarun na Kanar Gaddafi ke yi a yunkurin su na kwace birnin Misrata daga hannun 'yan tawayen rashin imani ne kuma ya saba ka'ida.

“Dakarun Kanar Gaddafi su kan kwabe kakin su su fake a rufin masallatai da asibitoci da makarantu.

“Nan ne inda suka girke manyan makamansu—kusa da masallatan da makarantun—sannan kuma suna yiwa kansu garkuwa da mata da kananan yara.

“Shi ya sa idan aka tamabaye ni me ya sa ba na komai sai in ce ni ba zan yi amfani da wadannan miyagun dabaru na yaki ba”.

A wata hira da ya yi da gidan talabijin na kasar Canada, CBC, Laftanar Janar Bouchard ya kuma ce dakarun NATO na kai hari a kan hanyoyin sadarwa na sojojin Gaddafi da rumbun makamansa.

Hafsan sojin na NATO, wanda dan kasar Canada ne, ya kuma ce dakarun sa sun lalata karin tankokin yakin Kanar Gaddafi guda biyu a kusa da birnin Misrata.

A halin da ake ciki kuma kimanin mutane dubu daya ne suka isa Benghazi daga birnin na Misrata.

An dai yi amafani ne da jirgin ruwa mai daukar manyan kaya wajen kwashe mutanen daga birnin wanda makwanni bakwai ke nan tun bayan da sojojin Kanar Gaddafi suka yi masa kawanya.

Mafi yawa daga cikin mutanen dai 'yan ci-rani ne daga kasar Ghana.

Karin bayani