Ana ci gaba da tattara sakamakon zaben Najeriya

Masu zabe a Najeriya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Masu zabe a Najeriya

A sassa daban-daban na Najeriya, ana can ana ci gaba da kidaya kuri’un da aka kada a zaben shugaban kasar da aka gudanar jiya.

A akasarin sassan kasar ta Najeriya dai an yi zaben ne cikin lumana, amma a wadansu wuraren an samu rahotannin tashin hankali.

Wadansu mutane wadanda suka sa ido a kan zaben na jiya sun ce sun amince da sahihancinsa musanman ma idan aka kwatanta shi da wadansu zabukan shugaban kasa da aka gudanar a kasar a baya.

Masu sa ido na kasashen duniya ma sun ce zaben ya gudana ba tare da tangarda ba, sai dai dan abin da ba a rasa ba.

Masu sa idon dai sun ce wannan zabe ka iya zama mafi sahihanci a cikin zabubbukan da aka taba yi a kasar cikin shekaru da dama, bisa la'akari da cewa a baya zabubbukan Najeriya kan gudana ne cikin tashin hankali da kuma murdiya.

Ga Shugaba Goodluck Jonathan dai babban kalubale a wannan zabe shi ne Janar Muhammadu Buhari na jam'iyyar CPC.

Karin bayani