An samu tashe-tashen hankula a Najeriya

Taron siyasa a Najeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Taron siyasa a Najeriya

An samu barkewar tashe-tashen hankula a wadansu sassan arewacin Najeriya, saboda rashin amincewa da sakamakon zaben shugaban kasar da aka bayyana ya zuwa wanda ke nuna cewa Shugaba Goodluck Jonathan ne ke kan hanyar samun gagarumar nasara.

Rikicin, wanda ya auku a jihohin Gombe, da Adamawa, ya kuma auku a jihohin Kaduna da kuma Sokoto bisa zargin cewa, anyi magudin da ya baiwa jam'iyyar PDP karin kuri'u.

Wakilin BBC a Jihar Kaduna ya bayyana cewa tarzoma ta barke ne a unguwannin biranen Kaduna da kuma Zaria, inda aka rika jin karar bindigogi cikin dare.

Rahotanni sun ce matasa sun yi ta kone-konen tayoyi yayin da jami’an tsaro suka yi ta kokarin tarwatsa su.

A Jihar Sokoto ma rikicin ya barke ne da misalin karfe tara na daren ranar Lahadi.

Rikicin ya biyo bayan zargin da matasa suka yi ne cewa jam’iyyar PDP ba ta samu yawan kuri’un da aka bayyana cewa ta samu ba.

Wakilin BBC ya ce matsan sun cinna wuta a kan duk wani gini mai dauke da alamar jam’iyyar ta PDP, da ma gidan rediyon Jihar, ko da yake an kashe wutar gidan rediyon kafin ta yi barna.

A kone-konen da aka yi a cikin garin Gombe kuma an lalata gidajen wadansu manyan ’yan siyasa na jam’iyyar PDP mai mulki domin wadanda suka aikata hakan su nuna fushinsu a kan magudin da suke zargin an tafka a zaben na shugaban kasa duk da cewa ’yan adawa ne suka yi nasara a Jihar.

An kuma kona wani otel da ake kira Old Maryland kamar yadda shaidu suka sanar da BBC.

Haka nan kuma mutane da dama ne bayanai suka ce imma dai an kashe su ko kuma an jikkata su a dauki ba dadi a garin na Gombe.

Kwamishinan ‘yansandan Jihar, Sulaiman Lawal, ya ce matasan ne suka janyo matsalar a matakinsu na ‘a-kasa-a-tsare kana lamarin ya ta’azzara.

A garin Bajoga hedikwatar karamar hukumar Funakaye ma dai an samu wani tashin hankalin inda bayanai suka ce matasa masu yawan gaske sun bazama a tituna suna kone-kone domin nuna adawarsu da sakamakon zaben da aka bayyana kana suka cinna wa wadansu gine-gine wuta.

Karin bayani