Buhari ya nesanta kansa da rikicin zabe

Dan takarar shugaban kasar Najeriya, Janar Muhammadu Buhari
Image caption Dan takarar shugaban kasar Najeriya, Janar Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya yi kiran a kawo karshen abin da ya kira ‘tashin hankali da kashe-kashen da basu dace ba’ a arewacin kasar, inda abokin hamayyarsa, Janar Muhammadu Buhari, yake da mafi yawan magoya bayansa.

Jonathan din dai ya yi wannan kira ne jim kadan bayan an bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar wanda aka gudanar ranar Asabar.

Shi ma dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar CPC ya mayar da martani game da rikicin, yana nesanta kansa da magoya bayan jam'iyyarsa daga rikicin.

“Wannan abin takaici ne da bai dace ba ko kadan—abin da ya faru abin Allah wadai ne wanda ba magoya bayan mu ba ne suka soma shi, kuma jam’iyyar mu ba ta goyon bayan abin da ya auku”, in ji Janar Buhari.

Rahotanni daga sassa daban-daban na arewacin kasar na cewa ma'aikatan tsaro sun shawo kan rikice-rikicen, inda wasu matasa suka bazama kan tituna suna kone-konen tayoyi, tare da kona gidaje da wuraren ibada a wasu sassa da kuma gidajen fitattun 'yan siyasa.

Matasan, wadanda akasarinsu 'yan shekaru sha-wani abu ne zuwa ashirin da-wani abu, sun datse tituna, inda a wadansu wuraren suke tilastawa mutane su amsa “Sai Buhari”, a yayin da a wadansu wurare kuwa, suka farma gidajen kiristoci.

A yau ne kuma ake sa ran kwamitin yakin neman zaben Janar Buharin zai yi zama na musamman.

Muhimman abubuwan da za su tattauna sun hada da yadda zaben shugaban kasar ya gudana da ma abubuwan da suka biyo baya.

Su ma malaman addinin Musulunci da na Kirista a jihar Kaduna sun nesanta rikicin da addini.

Sun dai bayyana hakan ne a wani taron gaggawa da suka kira na manema labarai ranar Litinin.

A cewarsu siyasa ce ta haifar da wannan rikici saboda haka kamata ya yi a bi hanyar siyasa wajen warware shi.

Jihar ta Kaduna dai na cikin jerin jihohin da a yanzu suke bin dokar hana fita, bayan rikicin da ya barke wanda kuma ya janyo asarar rayuka da dukiyoyi.

Karin bayani