Yau ne ake zaben shugaban kasa a Najeriya

Rumfar zabe a Najeriya
Image caption Rumfar zabe a Najeriya

A Najeriya yau ne miliyoyin mutane ke kada kuri'a a zaben shugaban kasa, wanda shi ne irinsa mafi girma a Afirka.

’Yan takara daga jam'iyyun siyasa goma sha tara ne suka shiga neman mukamin, cikinsu har da shugaban kasar mai ci, Dokta Goodluck Jonathan dan jam’iyyar PDP, ko da yake wadansu sun janye daga baya.

Manyan jam'iyyun da ke takarar ta yau dai su ne jam'iyya mai mulki ta PDP, da kuma jam'iyyun adawa kamar su CPC, da ANPP da ACN.

A kwanakin baya dai jam'iyyun CPC da na ACN sun yi yunkurin kulla kawance amma hakan bai yiwu ba.

Wadansu dai na ganin cewa da wuya a samu jam'iyyar da za ta yi wa sauran fintinkau, don haka zaben ka iya kaiwa zagaye na biyu a karo na farko a tarihin siyasar kasar.

Kimanin mutane miliyan saba’in da uku ne ake sa ran za su yi zaben na yau.

Sai dai zaben na cike da kalubalen tsaro.

A ranar Asabar din da ta gabata ma, an samu tashin bama bamai a lokacin da ake shirin zaben 'yan Majalisar Dokoki ta Kasa a garin Suleja, an kuma yi kashe-kashe a wadansu sassan kasar.

A jiya ma sai da wani bam din ya tashi a ofishin hukumar zabe da ke Maiduguri.

Mukamin Shugaban Kasa dai shi ne matsayi mafi daukaka a Najeriya don haka wannan zaben ke da muhimmanci.

Najeriya dai na cikin kasashen duniya masu arzikin mai, amma mafi yawan al'ummar kasar na fama da talauci saboda matsalar cin hanci da rashawa.