Ana ci gaba da samun sakamakon zabe a Najeriya

Ana ci gaba da samun sakamakon zabe a Najeriya
Image caption Har yanzu dai sakamakon na ci gaba da fitowa a sassan kasar da dama

A Najeriya ana ci gaba da samun sakamakon zaben 'yan Majalisun Dokokin da aka gudanar a ranar Asabar.

Wani abu da ya fito fili a zaben shi ne yadda ake samun sakamako daban-daban a sassa da dama na kasar.

Alal misali a yankin Kudu maso Yamma, jam'iyyar ACN ce kan gaba a sakamakon da aka bayyana kawo yanzu.

A yankin Kudu maso Gabas kuwa, jam'iyyar PDP ce a kan gaba, sai dai jam'iyyar APGA ma ta taka rawar gani a wasu mazabun.

A yankin Arewa maso Yamma kuwa, jam'iyyar PDP da CPC da kuma ANPP ne suke fafatawa da juna.

Alal misali a jihar Kano da Jigawa, PDPn ta lashe wasu mazabun da yawa, yayin da CPC da ANPP ma suka taka rawar gani.

Jam'iyyar PDP ta lashe kujeru biyu daga cikin uku na 'yan majalisar dattawa a Kano, yayin da ANPP ta lashe guda.

A jihar Katsina kuwa, rahotanni sun bayyana cewa jam'iyyar CPC ce a kan gaba.

Wannan ne dai karo na farko da jam'iyyun adawa ke baiwa PDP kalubale a wasu sassan da a baya ita ce ke da rinjaye.

Har yanzu dai sakamakon na ci gaba da fitowa a sassan kasar da dama.