Najeriya: An kai dare ana zabe a wasu rumfuna

Rumfunan zabe sun ci gaba da kasancewa a bude a wadansu sassan Najeriya har zuwa sa’o’in farko na safiyar yau Lahadi.

Wannan dai ya faru ne sakamakon yawan masu jefa kuri’a a ire-iren wadannan rumfunan wanda ya zarta adadin masu zaben da ya kamata a ce rumfa ta dauka.

Wakilin BBC ya ce har zuwa karfe goma sha biyu na daren jiya akwai inda ake ci gaba da jefa kuri’a a wadansu rumfunan zabe a babban birnin Jihar Kebbi, yayinda a wadansu rumfunan ake kidayar kuri’u a daidai wannan lokacin.

Wannan dai ya nuna irin jinkirin da za a iya samu wajen fitar da sakamako na karshe na zabubbukan a wannan yankin duk da an fara zaben cikin lokaci a akasarin wurare, kamar yadda wani mai sa ido a kan yadda aka gudanar da zaben ya shaidawa BBC.

Sai dai kuma wani abin da kusan kowa a wannan yankin ke farin ciki da shi shi ne yin zabubbukan cikin kwanciyar hankali da lumana in ban da ’yar hatsaniyar da ba a rasa ba.

Kafin zabubbukan na Majalisar Dokoki ta tarayya dai mutane da dama a ciki da wajen Najeriya sun yi ta bayyana fargabar cewa za a samu munanan tashe-tashen hankula a sassa daban-daban na kasar.

Hatta a jajiberin zabukan, hantar ’yan Najeriya da dama da ma wadanda ke zuci-zucin a yi zabubbukan kasar ta kada sosai, ganin yadda bom ya tashi a ofishin hukumar zabe a Sulejan Jihar Neja inda mutane da dama suka mutu.

Haka nan kuma wani abu ya fashe kana wasu ‘yan bindiga sun hallaka mutane a Maidugurin Jihar Borno; kafin wadannan ma a ranar Alhamis mutum guda ya rasa ransa a tashin bom a Kaduna.

Tuni dai mutane suka fara sharhi a kan yadda zabubbukan suka gudana lami lafiya a galibin sassan ksar ta Najeriya.

Malam Abubabakar Safiyanu Sa'id, wani mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum, ya shaidawa BBC cewa, “Babban abin da ya sa ba a samu tashin hankali ba, ina ganin tsarin da [hukumar zabe ta] INEC ta fito da shi ne.

“Da ma abin da ya ke kawo fada a wurin zabe, mafi yawa, shi ne yunkurin magudi—to wannan tsari da aka yi tsari ne da za mu iya kiransa na in-ka-ci-ka-ci”.

Su ma dai jami’an tsaro kusan murmushi suke yi baki har kunne kamar yadda kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Bauchi, ASP Muhammad Barau, ya bayyana:

“Mutane sun ba mu hadin kai; in ka ga yadda mutane suke layi abin sha’awa—wannan ya ba mu kwarin gwiwa kuma muna fatan zai dore”.

Yanzu dai an zuba ido a ga yadda mutane za su karbi sakamakon karshe na zabubbukan Majalisar Dokokin da kuma yadda za a tunkari zabubbuka na gaba.

Sai dai kuma wani abin da jama’a ke ci gaba da nuna damuwa a kai shi ne zargin rarraba makudan kudade ga masu jefa kuri’a a jihohi da dama.

A Gusau, babban birnin Jihar Zamfara, wadanda suka shaida lamarin sun ce a kan baiwa mai zabe kudi bayan an rataya masa Alkur’ani mai girma ya rantse cewa zai zabi jam’iyyar da ta ba shi kudin.

A Jihar Kaduna kuma an bayar da rahoton cewa an rarrabawa mutane kudi da wadansu kayyayki wadanda suka hada da taliyar Indomie, da sabulu, da sauransu.

Sai dai mutanen da suka zanta da wakilin BBC sun ce wannan ba zai sa su sauya ra’ayi ba.

Karin bayani