An kai harin bom a ofishin INEC na Suleja

Hoton harin da aka kai a Abuja ranar bikin samun 'yancin kai
Image caption A 'yan kwanakin nan an sha kai hare-haren bom a Najeriya

A Najeriya, wani abu ya fashe a ofishin Hukumar Zabe da ke Suleja a jihar Niger lokacin da malaman zabe ke karbar kayan zabe, wanda kuma ya yi sanadin mutuwar a kalla mutum biyu.

Harin ya kuma raunata wasu da dama, wadanda kuma aka garzaya da su wani asibiti a Sulejan.

Mafi yawan wadanda hadarin ya ritsa da su dai masu yi wa kasa hidima ne da aka dauka aikin zabe.

Hukumar zaben Najeriya da kuma Rundunar `yan sandan jihar Niger sun tabbatar da aukuwar lamarin.

Mahukuntan Najeriyar dai na zargin cewa abin da ya fashe din bom ne.

A watan Maris din da ya wuce ma wani bom din ya fashe a wajen wani taron siyasa a garin na Suleja, wanda ya kashe a kalla mutum hudu tare da raunana sama da mutum ashirin.