Rikicin Syria ya kara cin rayuka

masu zanga zanga a Syria Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption masu zanga zanga a Syria

Fiye da mutane ashirin ne suka rasu bayan da 'yan sanda suka budewa dubban masu zanga zanga wuta a garin Deraa dake Syria.

Akwai rahotannin dake cewa mutane da dama sun ji raunuka.

A wurin wata zanga zangar ma da aka yi a kasar, an bayyana cewa an jiyo karar harbe harben bindigogi a garin Hasrata:

Wakiliyar BBC tace akwai matukar damuwa a sauran sassan kasar, musamman ma da yake ba'a cikawa masu zanga zangar bukatunsu ba, sannan kuma abinda ya biyo bayan alkawuran da aka yi musu shi ne hari da jami'an tsaro ke kai musu da kuma karin kashe kashe.