Bankin Duniya ya nemi sauyi wajen ba da agaji

Hedkwatar Bankin Duniya
Image caption Hedkwatar Bankin Duniya

Wani rahoton Bankin Duniya ya bayar da shawarwarin kawo gagarumin sauyi a yadda ake tafiyar da harkar bayar da agaji ga kasashen duniya.

Rahoton ya ce kamata ya yi a rika bayar da muhimmanci ga karfafa hukumomi da kuma cibiyoyin da ke yin tasiri a kan rayuwar jama'a, domin idan ba a yi hakan ba da wuya a cimma kokarin shawo kan matsalolin kiwon lafiya da kuma ilimi.

A cewar rahoton hakan zai taimaka wajen hana barkewar rikice-rikice a maimakon tattara hankali wajen magance illolin da suka haifar.

Jigon wannan rahoto na Bankin Duniya dai zai zama wani gagarumin sauyi a yadda ake bayar da agaji ga kasashe ta yadda za a fi bayar da muhimmanci ga inganta aikin 'yan sanda maimakon gina sababbin asbitoci ko makarantu.