Kai Tsaye: Zaben 'yan majalisar dokokin Najeriya

Zaben Majalisar Dokokin Najeriya
Image caption Tantance masu kada kuria

Muna kawo muku bayanai kai tsaye dangane da yadda zaben 'yan majalisar dokokin Najeriya ke gudana a sassa daban-daban na Najeriya. Za ku iya aiko mana da bayanan yadda zaben ke gudana a yankunan ku ta e-mail a hausa@bbc.co.uk ko kuma ta dandalinmu na muhawara wato BBC Hausa Facebook. Za kuma ku iya aiko mana da hotuna da bidiyo ta wannan rariyar likau din: http://www.bbc.co.uk/hausa/yourpics/

19:35 A yanzu mun kawo karshen bayanan da muke kawo muku kai tsaye kan zabukan 'yan majalisar da aka gudanar a Najeriya. Sai ku kasance da mu a shirye-shiryenmu na rediyo da kuma intanet. A gobe ma muna nan dauke da wasu bayanan kai tsaye kan sakamakon zabukan da za a samu daga hukumar zabe a sassa daban daban na Najeriya.

19:27 Mu dai nan har an tada jannareto a akwati na 024 domin har yanzu ba'a gama kada kuri'a ba. Daga Sagir Adamu Compound Malumfashi.

18:55 Shugaban Hukumar zabe mai zaman kanta Farfesa Attahiru Jega, ya yabawa 'yan Najeriya game da yadda suka fito suka kada kuri'unsu. Kuma ya yi alkawarin tabbatar da gaskiya da adalci wajen bayyana sakamakon zaben da kuma shirya zabukan da ke tafe. Har ila yau Jega, ya yi Allah wadai da rahotannin da wasu kafafen yada labarai ke wallafawa na batanci kan hukumar, inda ya ce wannan ba zai taimakawa Najeriya ba.

18:35 Rahotannin da ke fitowa daga sassan Najeriya daban daban, na nuna cewa ana ta samun sakamakon zabukan da aka gudanar, amma muna jiran Hukumar INEC, ta fara bayyana sakamakon tukunna.

18:05 A yanzu rahotanni sun tabbatar da cewa mutum daya ne ya rasa ransa a harin bom din da ya faru a garin Maiduguri. Sabanin yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya rawaito.

17:57 Mu a garin Mayo Belwa har yanzu misalin karfe 5:47 na yamma, muna kada kuri'a komai na tafiya daidai. Daga Adamu Abubakar, Mayo Balewa Adamawa.

17:38 Mu a Kagoro Tudun Wada Kaduna. Ana nan ana kada kuri'a ba wani damuwa, an samu fitowa sosai musamman ma mata. Allah shi bamu nasara. Daga Muhd Bashir

17:28 Muna shaida muku za ku iya kallon hotuna da bidiyon yadda aikin tantance masu kada kuri'a da ma kada kuri'ar ya kasance a birnin tarayya Abuja. Sai ku je sashin hotuna da bidiyo a shafinmu na intanet wato bbchausa.com

17:19 A sakon da ya aiko mana ta facebook, Nazifi Umar cewa ya yi an fara zabe da misalin 1:15pm a mazabar Gwale da ke Yamma ward a Kazaure, jihar Jigawa. To amma duk da rashin farawar zaben da wuri yana tafiya lafiya ba tare da samun wata matsala ba.

17:06 A sakon da ya aiko mana ta Facebook, Umar Lawan ya ce babu shakka harkoki sun tafi tsaf a mazabar Gobirawa, Dala, Kano: Mazabar da ta fi kowacce yawa a jihar Kano. Godiya ta tabbata ga Allah da ya ba mu cikakken zaman lafiya.

1652 Rahatannin da muka samu sun nuna cewa duka manyan 'yan takarar shugabancin kasar - shugaban Goodluck na PDP da Janar Buhari na CPC da Nuhu Ribadu na ACN da Malam Ibrahim Shekarau na ANPP, duka sun kada kuri'unsu a mazabunsu daban daban.

16:47 A mazabar mu ta filin Sale a Karamar Hukumar Jibia, an kammala zabe, domin nine mutum na karshe da ya kada kuri'ar shi, yanzu haka ga shi nan ana kidaya a gaban kowa. In ji Muhd Sayyadi Jibia.

16:41 Rahotannin da muke samu daga wasu sassan Najeriya na cewa an fara kammala zaben a wasu wurare tare da kirgawa da kuma bayyana sakamako a wasu mazabun.

16:39 A sakon da ya aiko mana daga Jalingo Bashir Adamu, ya ce zabe na guda kamar yadda ake so a mazabar kasuwar Yalwa. Sai dai matsalolin da ba'a rasaba kamar: Rashin cikakkun takardun kada kuri'a, yawan mutanen da aka tantancesu sun fi karfin takardun kada kuri'ar da aka kawo mazabun. Haka kuma rashin sauri a wajen ma'aikatan INEC na wucin gadin dake aiki. Babu wani tashin hankali, jami'an tsaron suna zaune su nata hira da mutane.

16:10 Masana da dama na ganin an samu ci gaba sosai idan aka kwatanta da zabukan da aka gudanar a Najeriya a baya.

15:59 Kamfanin dillancin labarai na AP, ya ce wakilinsa da ya ziyarci asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri, ya ga akalla gawarwakin mutane 10 da suka rasa rayukansu a harin bom din da aka kai a garin Maiduguri na Jihar Borno. Sai dai har yanzu jami'ai na cewa ba su samu labarin wanda ya rasa ransa ba.

15:43 A sakon da Inuwa Awwal ya aiko mana ta adreshin e-mail, cewa ya yi shakka babu mutane basu bada hadin kai wajen futowa a wannan satinba, musamman idan aka kwatanta da satin da ya wuce a nan mazabar Zaitawa Kano Municipal, amma shakka babu komai yana tafiya Daidai... Allah ya zaba mana mafi alkhairi, Ameen.

15:16 A bayanin da ya wallafa a shafinmu na Facebook, Muhammad Basheer Muhd ya ce a garin Azare na Jihar Bauchi an fara kada kuri'a a wasu mazabun da misalin 2:00pm amma a wasu mazabun har yanzu ana tantancewa. Ko me ya kawo wannan jinkiri duk da cewa an fara tantancewa da misalin karfe 8:00 na safe?

14:49 Muna shaida muku cewa a yau shirinmu na rana zai fara ne daga karfe uku zuwa biyar na yamma, inda za mu kawo muku bayanai da sharhi kan abubuwan dake faruwa daga sassan Najeriya daban daban.

14:41 A bayanin da ya wallafa ashafinmu na facebook Sade Saidu Daura, cewa ya yi "Jama'a mu kara hakuri da shan rana da muke yi. Nan gaba kadan za mu shiga inuwa idan muka zabi wakilai nagari".

14:12 A bayanin da ya wallafa a shafinmu na FacebookSamaila Zagga, cewa ya yi Alhamdu lillahi, mu dai anan garin Zagga na karamar Hukumar Bagudo a jihar kebbi. Zabe na gudana duk yadda ya kamata. Allah yasa haka abin yake ko'ina a Najeriya.

13:49 Sani Halle ya rubuta a shafinmu na Facebook cewa, wai don Allah ina dokar da hukumar zabe ta sanya ta kama duk wanda ya bada kudi a rumfar zabe? Gaskiya wannan doka bata aiki a mazabu da yawa.

13:32 Za ku iya aiko mana da bayanai da hotuna dama bidiyo kan abinda ke faruwa a yankunanku ta adreshinmu na email a bbchausa.com, ko kuma ta dandalinmu na BBC Hausa Facebook, wanda za ku iya samu a bbchausa.com

13:28 Har yanzu ba a samu damar fara kada kuri'a a mazabar Maitama 024 a Abuja ba, saboda wadanda ba su ga sunansu ba, sun ce ba za ta sabu ba. Sai dai jami'an tsaro sun isa wurin nan take. Kamar yadda Aliyu Dalhatu ya shaida mana.

13:23 Kamar yadda ya wallafa a shafinmu na BBC Huasa facebook, Abdulsalam Ya'u TelaNguru cewa ya yi har yanzu 13:18 a garin Nguru na jihar Yobe a mazabar Bage Najajuwa da ke Sabon Garin Kanuri ba a gama tantancewaba balle mu fara zabe.

13:18 Rahotannin da muke samu daga sassa daban-daban na Najeriya na nuna cewa zabe na tafiya yadda ya kamata, inda jama'a ke ci gaba da kada kuri'unsu bayan an tantance su.

13:13 A bayanin da ya wallafa a shafinmu na BBC Huasa Facebook, Sani Hassan Dutsin-ma ya ce a mazabarmu ta Abacha Estate dake Abuja zabe yana tafiya kamar yanda ya kamata, sai dai kimanin mutum 90 basu sami sunayensu ba, amma mun kai kukanmu ga Hukumar INEC muna fatan za su duba su yi gyara.

13:04 Aliyu Ahmad Ali Gorondo ya rubuta a shafinmu na Facebook cewa: Mu kan a unguwar Dawaki jihar Bauchi sai hamdala, ana jefa kuri'a yadda ya kamata. Allah ya sa abunda muka zaba ya zama alkairi.

13:02 Wakilinmu na yankin Naija Delta Abdul Muhammad Isa ya aiko mana da bayanin cewa an samu harbe-harbe a yankin Ekeremor da Sagabama na jihar Bayelsa. Bayanai da ba a tabbatar ba sun ce harbe-harben sun auku ne tsakanin mutanen da ke yunkurin satar akwatu da takardun kada kuri'a.

12:56 Domin kallon hoton bidiyon yadda aikin tantance masu kada kuri'a ya gudana a birnin tarayya Abuja, sai ku latsa wannan rariyar likau din http://www.bbc.co.uk/hausa/multimedia/2011/04/110408_mpselection_video.shtml

12:49 A jawabin da ya wallafa a shafin mu na Facebook, Alh Sani Abba ya ce an fara zabe karfe da misalin 12:40 a akwatin 06 hudu a mazabar Rumfa a Hadeja komai yana tafiya daidai.

12:46 Rahotanni na cewa a kalla mutane bakwai ne suka rasa rayukansu a sassa daban daban na kasar. A jihar Osun, an kashe mutane hudu a wata majami'a. Yayin da mutum guda ya mutu a yankin Naija Delta, lokacin da rikici ya barke tsakanin matasan da suka yi kokarin kwace kayan zabe a yankin Ekeremor inda aka ji harbe-harben bindiga a makon da ya wuce.

12:38 A mazabar Layin Kosai Tudun Wada Kaduna an gama tantancewa amma ba jami'an tsaro kuma ma'aikata sun ce baza a fara kada kuri'a ba sai Jami'an tsaro sun zo. Daga Aleeu Mohermmed Toorerkee.

12:35 Wakiliyar mu a Maiduguri Bilkisu Babangida ta ce Bom din da ya tashi dazu a garin ya tashi ne a rumfar zaben Maidokiri, kuma mutane da dama sun jikkata.

12:31 Gwamnan jihar Legas Babatunde Fashola, ya yabawa Hukumar zabe kan yadda ta shawo kan matsalolin da aka samu a makon da ya gabata, sai dai ya koka kan yadda jama'a ba su fito kamar makon da ya wuce ba. Gwamnan yana magana ne a lokacin da ya je mazabarsa domin a tantance shi.

12:27 A mazaba ta 024, a unguwar Maitama da ke birnin tarayya Abuja, wasu da ba su ga sunayensu ba, sun hana a fara kada kuri'a, suna cewa sai an nemo sunayensu an tantance su tukunna. Daga Aliyu Dalhatu Jama'are.

12:23 Rahotanni daga Maiduguri na cewa wani abu da ake kyautata zaton Bom ne ya tashi a unguwar Maidoki, kuma mutane da dama sun jikkata. Za mu kawo muku karin bayani nan gaba.

12:19 Gaskiya zabe yana tafiya yadda ya kamata sai dai matsalar mu ita ce wasu hotunan basu fito sosai ba ta yadda za'a iya tantance wanda yake jikin rajistar, sannan matsala ta gaba ita ce rashin ganin sunayen wasu a cikin littafin tantance masu zabe. Daga Sani Muhammad Karamar Hukumar Fagge Kano.

12:17 Kassim Abubakar Gamawa ya rubuta a shafinmu na Facebook cewa, yanzu haka an gama tantance masu kada kuri'a a nan garin Gamawa lami lafiya. Allah ya sa a gama zaben ma lafiya.

12:15 A jihar Adamawa an kama wadansu mutane da kuri'a masu yawa kuma da alama ba bisa ka'ida aka samu wannan kuri'u ba, yanzu haka suna hannun jami'an tsaro ana bin cike kan wannan lamari. Daga Abba Ahmad Yola.

12:12 A karamar Hukumar Jibia, jihar Katsina, 'yan siyasa na sheke ayar su a rumfunan zabe, ta hanyar bada kudi ga masu kada kuri'a duk da jami'an tsaron dake rumfunan. Inji Muh'd Sayyadi Filin-Sale, Jibia, Katsina.

12:10 Abdussalam Ibrahim Ahmed a Enugu ya ce mutane sun fito sosai domin a tantance su su kada kuri'a a wasu wuraren, yayinda a wasu wuraren aka samu raguwar zumudin zaben ba kamar makon da ya gabata ba. Sai dai ya ce an samu ingancin tsaro fiye da makon da ya gabata a garin.

12:05 A jihar Kano abokin aikinmu Mansur Liman ya ce komai na tafiya yadda ya kamata ba tare da wata matsala ba, mutane na ta ikirarin neman sauyi, sai dai ba a san me irin wannan sauyin zai haifarba.

12: 02 Mu yanzu anan mile12 Lagos abubuwa na tafiya yadda ya kamata mutane da dama sun fito musammam ma Hausawa da yake sune mafi rinjayen mazauna yankin. Sako daga Bash Control Kano.

11:59 Abdul Muhammad Isa a yankin Naija Delta ya ce a yankunan da ya zagaya a jihar Rivers, mutane na kan layi ana ci gaba da tantance su. Sannan mutane sun fito da kujeru, ba sa tafiya gida bayan an tantance su. Su ma sun kasa sun tsare.

11:55 Yanzu misalin karfe 11:34 na rana, A mazabata dake garin gamawa a jihar Bauchi komai ya kankama, domin kuwa har an kammala tantace masu kada kuri'a. Daga Kamisu Shehu Jazuli Gamawa Jihar Bauchi.

11:50 Wakiliyar mu Bilkisu Babangida a Maiduguri, ta ce zabe na gudana yadda ya kamata a mazabun da ta zagaya zuwa yanzu. Mutane sun fito fiye da makon da ya gabata. Wasu rumfunan da ta je sun gama tatancewa suna jiran kada kuri'a ne ma yanzu. Bilkisu ta ce a wasu mazabun ma an shimfida manyan tabarmu ne mutane suna jiran lokacin kada kuri'a ya yi. Mutane suna nuna farin cikinsu dangane yadda al'amura suke tafiya. An dai tsaurara matakan tsaro a garin.

11:49 An samu tashe-tashen hankula a sassa da dama gabanin wannan zaben, inda wasu 'yan bindiga suka kashe wani dan siyasa a jihar Borno da ake Arewacin kasar. Wannan zabe dai na da matukar mahimmanci ganin irin makudan kudaden da 'yan majalisar kasar ke karba, wadanda kididdiga ta nuna cewa sun kai kusan naira miliyan guda a kowanne wata.

11:41 An samu wani malamin zabe da yunkurin sayar da takardun zaben ga wata jam'iyya a mazabar Majema, da ke karamar Hukumar Hadeja. Amma 'yan sanda sun yi awangaba da shi. Mun samu bayanin ne daga mai saurarenmu Malam Daudu.

11:39 Tabbas tsaro wurin zabe yayi amma kash! Wajen tantacewar nan, ina ma za'a dinga tantancewa kwana daya kafin ranar zabe, da an rage bata lokaci a wajen yin zaben. Sakon hadin gwiwa daga Ahmad Mu'awiya Umar da Bashir Garzali a Ringim jihar Jigawar Nigeria.

11:39 Mu dai ba mu san me hukumar zabe ke nufi ba saboda ana samun kura kurai a wajen zabe. Mutane sun fita wajen yin zabe amma abin takaici sai kabi layi ka bata lokaci fiye da awa biyu sai layi yazo kanka sai a duba sunanka a rasa. In ji Ibrahim l Ibrahim, Birnin Kudu Jigawa

11:37 Ku latsa wannan rariyar likau din don kallon hotunan yadda ake tantance masu kada kuri'a: http://www.bbc.co.uk/hausa/multimedia/2011/04/110408_mps_elections.shtml

11:36 A gaskiya masu kada kuri'a a mazabar mu ta Karofi Keffi basu fito sosai ba kamar satin da yawu ce. Ina ga akwai dalilai uku. 1. Dakatar da zaben da aka yi makon da wuce. 2. Rashin yin zaben 'yan majalisar wakilai ta tarayya. Rashin kakkarfar adawa tsakanin 'yan majalisar sanatoci. Wadannan ina ganin sune dalilai kwarara da suka sa masu kada kuria ba su fito sosai ba. In ji Yusuf Abdullahi, Keffi

11:35 Nayi mamakin yadda al'ummar Najeriya suka fito kwansu da kwarkwatar su don zaben wakilai na kwarai, wadanda za su ciyar da kasar mu gaba. Koda yake a fahimta ta, kin fitowa yin zabe da al'ummar Najeriya ke yi, ya samo asali ne daga zabe nagari da suke ana basu gurbatacce, amma a wannan karon muna yi wa hukumar zabe kyakkyawan zaton ba zata bari a yi amfani da ita kamar yadda aka yi a baya ba. Muna fatan samun abinda muka zaba don kasarmu ta zauna lafiya. In ji Kabir sakaina Layin 'yangoro Malumfashi.

11:34 Mudai mutanen unguwar Kakabori Hadejia sai dai mu ce Alhamdulillahi domin tun kafin lokacin da hukumar zabe ta kayyade, aka fara tantance mutane. Wato tun misalin karfe bakwai da kwata domin gudun bata lokaci. kuma yanzu haka aikin yana tafiya babu matsala. Sako daga Babangida chairman Kakabori Hadejia jihar Jigawa.

11:33 A yau ne mu talakawa ake tantance mu a layin zabe. Muna sa rai da gudanar da zabe yau in Allah Ya yarda. In ji Telah mai oil, Adamawa.

11:31 Wakilinmu Haruna Shehu Tangaza a Zamfara ya ce wasu matasa sun gudanar da zanga- zanga a hedikwatar 'yan sandan jihar, inda aka kame wasu matasa da aka ce sun shigo daga Sokoto don yiwa wata jam'iyya wakilan zabe. Haruna ya ce zabe na tafiya yadda ya kamata, kuma kayan aiki sun isa mazabu da dama a kan kari. Jama'a kuma sun fito amma ba kamar makon da ya gabata ba. Idan an tantance mutane kuma suna zama ne ba sa tafiya gida.

11:19 A sakon e-mail da ya aiko mana Auwal Kazaure City cewa ya yi: Mu talakawan jihar Jigawa mu yi hattara domin wasu sun fito da kazaman kudi suna rabawa.

11:18 Wakilinmu Nura Ringim a Kaduna ya zagaya wasu mazabu a garin na Kaduna. Ga misali a Kurmin Mashi, akwai mazabu da dama da ba su ga jami'an zabe ba har zuwa karfe goma na safe maimakon karfe takwas da aka ce za a fara tantance masu kada kuria. Sai dai a mazabun da jami'an suka fito, akwai cunkoson jama'a. A Unguwar Sanusi, Nura ya ce jami'an zabe ba su je ba sai wajen karfe tara da rabi. A Unguwar Rimi kuwa ya tarar ana tantance jama'a. Badikko kuwa Nura ya tarar da cunkoson jama'a a akwatuna da dama.

11:07 Mu dai a jihar Adamawa kayan zabe sun isa ko ina da ko ina. In ji Umaru Mai kayan chasu Malabu a sakon da ya aiko mana ta wayar salula.

11:04 Wakilinmu Yusuf Ibrahim Yakasai a Kano ya ce aikin tantance masu kada kuri'a na tafiya yadda ya kamata a mazabun da ya zagaya. Kuma wasu mutanen idan an tantance su suna tafiya gida ne da zummar za su dawo karfe sha biyu da rabi lokacin da za a fara kada kuri'a.

10:52 Muhammad Ibrahim Daga Wuse Zone 4 Abuja ya ce, Mun yi rajista amma an ce babu sunan mu a rajista. Idan ba mu samu mun yi zabe ba yanzu yaya za a yi a zaben shugaban kasa?

10:45 Mun tashi da hazo-hazo ba rana, kuma jama'a sun fito domin su kasa su tsare kuri'ar su. A yanzu an tantance ni kuma an bani lamba ta 57. Muna jiran a fara kada kuria. Yakubu Futuless daga Michika jihar Adamawa