Kwashe ma'aikatan Birtaniya a Abidjan

An kwashe ma'aikatan ofishin jakadancin Birtaniya dake birnin Abidjan na kasar Ivory Coast, sabilida fadan da ake tabkawa tsakanin dakarun da ke biyayya ga mutanan dake kokawar shugabancin a kasar.

Kwashe ma'aikatan ya biyo bayan harba harsasai kan ginin da kuma makaman igwan da suka fada cikin harabar ginin.

Ofishin jakadancin Birtaniyan na kusa da fadar shugaban shugaban kasar ne inda Laurent gabgbo mutumin da ya ki sauka daga mulki ya ke zaune.

A waje daya kuma jami'an MDD sun tabbatar da cewa dakarun Mr. Gbagbo sun harba makaman igwa wajen Golf Otel, inda abokin hamayyarsa Alassane Outtara ke zama.