Dakarun Gaddafi a Ajdabiyya

Dakarun dake biyayya ga Kanal Gaddafi sun kaddamar da hari a garin Ajdabiya dake gabashin kasar Libya, wajen da ke karkashin ikon 'yan adawa.

Dakarun gwamnatin sun yi lugudan wuta a kan garin, inda aka kwashe sa'o'i ana ta ana ta bata kashi.

Wani wakilin BBC yace harin ya zowa 'yan tawayen da bazata.

GIdan talabijin na gwamnatin Libya ya nuna hotunan bidiyon dakarun gwamnatin na ta daga tutocinsu a garin.