Ana ci gaba da kirga kuri'u a Nigeria

Masu zabe a Nigeria
Image caption Masu zabe a Nigeria

A Najeriya, an kammala zaben `yan majalisar dokokin kasar da aka fara tun da safe, kuma ana can ana ci gaba da kidayar kuri`un.

Kamar yadda hukumar zaben kasa ta yi alwashi, an kyale masu zabe sun tsaya a mazabu don ganin yadda ake kidaya kuri`unsu.

Hukumar zaben kasar dai ta yi alkawarin sanar da sakamakon zabukan, wadanda suka hada da na `yan majalisar dattawa da na wakilai a cikin kwanaki biyu.

Zamu leka sassa daban daban na Nijeriya, domin jin irin wainar da aka toya, a lokacin wannan zabe da ma kuma bayyana sakamako.