An kama shugaba Gbagbo na Ivory Coast

Laurent Gbagbo
Image caption An shafe makwanni ana tafka kazamin fada kafin kama Gbagbo

An kama tsohon Shugaban Ivory Coast, Laurent Gbagbo -- wanda ya ki ya bayar da mulki ga abokin hamayyarsa, Alassane Ouattara.

An kama shi ne jim kadan bayan da dakarun Faransa da mayakan Alassane Ouattara suka karaci gidansa, sannan suka dauke shi zuwa Otel din da Alassane Ouattara yake zama a Abidjan.

Daga bisani dai wani gidan Talabijin mai goyon bayan Alassane Ouattara ya watsa wani sako daga Mr Gbagbo yana kira da a kawo karshen tashin hankali.

Sakatare Janar na Majalisar dinkin duniya, Ban Ki Moon ya ce zai tuntubi Alassane Ouattara domin tattaunawa kan yanayin halin da jama'a suke ciki a Ivory Coast.

Kace-Nace

Akwai bayanai masu saba wa juna dangane da yadda aka kama Mr Gbagbo.

Jakadan kasar Faransa ya ce sojojin da ke biyayya ga Mr Outtara ne suka kame shi, yayinda wani mataimaki ga Gbagbo ya ce sojoji na musamman na kasar Faransa ne suka kama shi.

Sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya, sun ce Gbagbo yana jefa rayuwar fararen hula cikin hadari, sannan suka nemi sojojin Faransa su dauki mataki kan domin kare fararen hula.

Sai dai wata majiya ta Faransa ta musanta cewa dakarun kasar ne suka kama Gbagbo.

"Tabbas dakarun Ouattara sun kama Mr Gbagbo, amma ba dakarun Faransa na musamman ba, wadanda ba su shiga bukkar da Gbagbo ya ke ba," kamar yadda majiyar ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.