PDP na fuskantar kalubale a zaben shugaban kasa

Masu zabe a kan layi Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Masu zabe a kan layi

Koma bayan da jam'iyyar PDP mai mulki ta samu a zabukan 'yan majalisar dokoki na kasa na nuni da cewa dan takarar ta na shugaban kasa Goodluck Jonathan ka iya fuskantar kalubalai mai girma a zaben shugaban kasa.

Sakamakon da aka samu i zuwa yanzu na nuni da cewa a yanzu jam'iyyar PDP na da rinjaye mai rauni ne a majalisar dokokin.

Akwai dai manyan 'yan jam'iyyar PDP mai mulkin da suka sha kasa a zaben, ciki kuwa har da kakakin majalisar wakilai ta kasa, Dimeji Bankole, da kuma 'yar tsohon shugaban kasar Iyabo Obasanjo wadda ta rasa kujerarta ta 'yar majalisar dattijai.

Jam'iyyar PDPn ta kuma samu koma baya a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya, jihar da mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo ya fito, wanda yana cikin wadanda jam'iyyar ta dogara da su don kawo mata kuri'un 'yan arewacin kasar a zaben shugaban kasa.

Kaka-Gida

Tun bayan kawo karshen mulkin soja a kasar a shekarar 1999, jam'iyyar PDPn ce ta mamaye siyasar Najeriya - kasar da ta fi kowacce yawan jama'a a nahiyar Afrika.

Dan takarar ta ne ke lashe zaben shugaban kasa, kuma ita ke iko da mafi yawan jihohi 36 na kasar dama majalisar dokoki ta kasa.

Sai dai tun shekarar 1999, Najeriya ba ta gudanar da zabe mai inganci ba, kuma ganin cewa a karon farko jam'iyyar PDP mai mulkin kasar na fuskantar gagarumin koma baya, ka iya bawa jam'iyyun da ma al'ummar kasar karfin gwuiwar cewa za su iya kada jam'iyyar a zaben shugaban kasa.

Da dama daga cikin masu sa ido a kan zaben kasar na da ra'ayin cewa, akwai yiwuwar jama'ar da za su fito a zaben shugaban kasa su dara wadanda suka fito a zaben 'yan majalisar kasa.

Majalisar Dokoki

Sakamakon zaben majalisar dokokin kasar da aka gudanar ranar Asabar dinda ta gabata ya nuna cewa, za a samu majalisa wadda take da mabanbantan jam'iyyu masu fada a ji, kuma hakan in ji masu sharhi zai karfafa mulkin demokradiyya a kasar.

Sai dai wasu na ganin cewa irin hakan ka iya kawo koma baya ga tafiyar demokradiyyar kasar, ta hanyar kawo jinkiri wajen zartar da kudurorin doka, sabanin yadda lamarin yake a lokacin da PDP ke da gagarumin rinjaye.

Hukumar zabe

Duk da cewa an yaba da kokarin da hukumar zaben kasar ta yi wajen gudanar da zaben 'yan majalisar dokokin da ya gabat, an ci karo da wasu matsaloli.

Kazalika an yi zargin cewa wasu sun yi amfani da kudi wajen sayen kuri`a.

Yadda zaben `yan majalisar dattawa da na wakilai ya gudana a ranar Asabar din da ta gabata dai za a iya cewa ya kara wa hukumar zaben Najeriya tagomashi a idon `yan kasar da dama da kuma kasashen duniya.

Hatta majalisar dinkin duniya da masu sa-ido a kan zaben na kasa-da-kasa sun yaba da kamun-ludayin hukumar zaben.

Sai duk da sambarkar da ake yi wa hukumar zaben, an fuskanci wasu matsaloli mazabun kasar a lokacin zaben, da suka hada da bacewar sunayen wasu masu kada kuri`a da kuma sace-sacen akwatunan zabe a nan da can, da kuma jinkirin isar kayan zabe a wasu mazabu kalilan.

Har ma da zargin da wasu ke yi na amfani da kudi a ranar zabe wajen saye kuri`un jama`a.

Ganin cewa zaben `yan majalisar dokokin Najeriyar kamar sharar-fage ne ga sauran zabukan da ke tafe, musamman ma idan aka kwatanta da zaben shugaban kasar da ke biye, ga dukkan alamu hukumar na da jan aiki na kara shiri don kauce wa matsalolin da ta fuskanta a baya.

Daraktan hulda da jama`a na hukumar Mr Nick Dazang ya ce hukumar na kara shiri sosai don tunkarar zaben shugaban kasa da ke tafe a kasar.

Masu lura da al`amura dai na ganin cewa akwai bukatar hukumar zaben ta kara jan-damara, saboda suna hasashen cewa akwai yiwuwar yawan masu zabe a zaben shugaban kasa zai zarta wanda aka gani a zaben `yan majalisar dokokin kasar.