Sabuwar girgizar kasa a Japan

An sake samun wata girgizar kasa a Japan a dai dai lokacin da ake cika wata guda cur bayan mummunar girgizar kasa ta tsunami ta yi matukar barna a arewa maso gabashin kasar.

Girgizar kasar data abku da girmanta yakai maki 7.1 ta faru ne a wani wuri dake kudancin tashar makamashin nukiliya ta Fukushima wacce ta lalace a watan daya gabata.

Tun da farko a yau ne Pira Ministan Japan, Naoto Kan ya jagoranci jami'an gwamnatinsa wajen yin addo'i ga wadanda suka rasu a bala'in girgizar kasar.