An kama shugaba Gbagbo na Ivory Coast

Laurent Gbagbo
Image caption An shafe makwanni ana tafka kazamin fada kafin kama Gbagbo

An kama tsohon shugaban kasar Ivory Coast, Laurent Gbagbo, wanda ya ki mika mulki ga abokin hamayyarsa, Alassane Outtara.

Jami'an ma'aikatar tsaron Faransa sun ce dakarun Mr. Outtara dake da goyan bayan Majalisar Dinkin Duniya da Faransa na tsare da shi.

Tun da farko dakarun sojin sun kutsa kai cikin gidan da Mr. Gbagbo ya buya na karkashin kasa.

Yanzu haka an kai shi tare da matarsa da dansa otel din da dakarun Majalisar Dinkin Duniya ke gadinsa, wato Golf Otel

Jakadan Ivory Coast a Mjalisar Dinkin Duniya ya ce Mr Gbagbo na nan lafiya lau da ransa kuma za'a hukunta shi.

Kace-Nace

Akwai bayanai masu karo da juna dangane da yadda aka kama Mr Gbagbo.

Jakadan kasar Faransa ya ce sojojin da ke biyayya ga Mr Outtara ne suka kame shi, yayinda wani mataimaki ga Gbagbo ya ce sojoji na musamman na kasar Faransa ne suka kama shi.

Sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya, sun ce Gbagbo yana jefa rayuwar fararen hula cikin hadari, sannan suka nemi sojojin Faransa su dauki mataki kan domin kare fararen hula.

Sai dai wata majiya ta Faransa ta musanta cewa dakarun kasar ne suka kama Gbagbo.

"Tabbas dakarun Ouattara sun kama Mr Gbagbo, amma ba dakarun Faransa na musamman ba, wadanda ba su shiga bukkar da Gbagbo ya ke ba," kamar yadda majiyar ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.