Japan ta daga ma'aunin barnar nukiliya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jamian hukumar da makamashin nukliya a Japan

Gwamnatin Japan ta daga ma'aunin barnar da tashar nukliyar Fukushima ta fuskanta zuwa bakwai, ma'auni mafi girma, idan aka kwatanta da yadda ake auna barna a duniya.

Hukumar dake kula da makamashin nukliyar kasar, ita ce ta tabbatar da haka bayanda kafofin yada labarun kasar, suka yi ta bada rahotanni game da wanan batu

Mahukunta Japan sun kwatanta lamarin da ya auku a tashar Fukushima da balainda aka yi wa lakabi da Chernobyl da ya auku a shekarar 1986.

Sai dai sun ce babu wani abu da ke nuni da cewa wanan mataki nada nasaba da jerin girgiza kasa me karfin gaske da suka auku a baya baya nan.