Za'a fara sharia akan Laurent Gbagbo

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Mr Laurent Gbagbo

Mutumin da kasashen duniya suka dauka a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar Ivory Coast, wato Alassane Ouattara, ya ce za a fara sharia kan abokin adawarsa Laurent Gbagbo.

Mr Ouattara na magana ne, sao'i bayanda a karshe Mr Gbagbo yayi saranda ga dakarunda suka yi masa kawanya a gidansa dake Abidjan, bayan shafe watanni hudu, da yin kememe akan shugabancin kasar.

Mr Watara dai ya bada tabaccin cewa za'a kare lafiyar Mr Gbagbo sai dai ya ce ya nemi ministan shariar kasar akan ya fara gudanar da bincike akan Mr Gbagbo , matarsa da kuma sauran mutanen da suka taka rawa a rikicikin siyasar kasar.

Ya kuma ce za'a kafa wani kwamitin sulhu da zai tattara bayanai akan abun da ya kira miyagun laifuka da kuma toye hakin biladama da suka auku a lokacin rikicikin.