Kawancen ACN da CPC na tangal-tangal

jam'iyyar ACN
Image caption Jam'iyyar ACN ta yi rawar gani a zaben ranar Asabar

A Najeriya, da alama samun wata jarjejeniya tsakanin manyan jam'iyyun adawa na kasar biyu wato ACN da CPC kafin zaben shugaban kasar da za'a yi ranar Asabar mai zuwa na tangal-tangal.

Yau kwanaki biyu kenan da jam'iyyun suke tattaunawa domin ganin sun fitar da dan takara daya da zai kalubalanci shugaba Goodluck Jonathan na jam'iyyar PDP, amma jam'iyyun ACN da CPC sun tashi ba tare da cimma yarjejeniya ba.

Dukkanin jam'iyyun sun yi hira da manema labarai daban-daban inda suka bayyana cewa har yanzu basu fitar da tsammanin yin kawance anan gaba ba.

Sai dai rahotanni sun bayyana cewa akwai yiwuwar Malam Ibrahim Shekarau na jam'iyyar ANPP ya janyewa Janar Buhari na CPC.

Batun da ake shi ne na malam Nuhu Ribadu na ACN, ya janye wa Janar Buhari na CPC, domin tunkarara Jonathan.

Yayin da ACN za ta mika sunan Fola Adeola, a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa.

Wani batun kuma shi ne na Riabdu ya ci gaba da takararsa, amma zai kulla kawance da Buhari idan aka kai zagaye na biyu.

Jam'iyyar PDP ta lashe dukkan zabukan da aka yi, tun bayan da kasar ta koma tafarkin dimokuradiyya, sai dai jam'iyyun adawa na fatan za su tilastawa PDPn zuwa zagaye na biyu.

Zaben makon da ya gabata

A zaben ranar Asabar din da ta gabata, inda ACN ta samu karin kujeru a yankin Kudu maso Yamma, amma CPC ta kasa kai bantanta kamar yadda ka yi tsammani - abinda ya kara cakuda lamarin.

Jam'iyyar PDP wacce ta mamaye fagen siyasar kasar, ta rasa kujeru da dama a zaben na ranar Asabar.

Rinjayen da take da shi a majalisar wakilai zai haura rabi ne da kadan - maimakon kashi uku cikin hudu a baya.

Shugaba Jonathan na bukatar samun gagarumin rinjaye da kuma kashi 25 cikin dari a biyu bisa uku na jihohin kasar domin lashe zaben a karon farko.

Sai dai masana na ganin samun hadin kai domin kawar da Jonathan a wannan kurarren lokacin abu ne mai wahala.