'Yan tawayen Libiya zasu sami taimakon kudi

Taron Doha a kan Libiya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Taron Doha a kan Libiya

Wakilan kwamitin tuntuba na kasashen dake adawa da gwamnatin Kanar Gaddafi a Libya, sun amince su bullo da wata hanya, wadda zata samar da gudunmawar kudi ga 'yan tawayen kasar Libyar.

Wata sanarwa da aka fitar bayan taron da aka gudanar a Qatar ta ce, za a yi amfani da gudunmawar kudin ce, wajen magance matsalar kudi, da kuma samar da wasu kayan aikin da 'yan tawayen suke bukata.

Sai dai kasashen ba su bayyana ko za a iya amfani da kudin wurin sayen makamai ba.

Sanarwar ta kara maimaita kiran cewa sai Kanar Gaddafi ya sauka daga mulki, domin ba shi da halaccin ci gaba da jan ragamar mulkin kasar.