Amurka ta yi Allah wadai da Gwamnatin Libya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Hilary Clinton

Gwamnatin Obama ta yi Allah wadai da abinda ta kira sabbin miyagun laifukan da dakarun dake biyayya ga Kanar Gaddafi ke aikatawa a kasar Libya.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hilary Clinton, ta ce mayakan haya na kanar Gaddafi sun kai hari kan fararen hula a birnin Misurata dake yammacin kasar.

Ta ce su na harba bama bamai a unguwannin fararen hula, kuma maharba na kai hari kan fararen hular da suka jikkata.

Sai dai ana ganin cewa kalaman da suka fito daga bakin Amurkan watakila wani gargadi ne da aka shirya domin a shawo kan wasu kasashen dake kungiyar NATO, da Birtaniya da Faransa ke zarginsu da rashin aiwatar da wani abun a zo gani dangane da yakin Libya.

Bugu da kari wasu a Amurkan na ganin cewa ya kamata gwamnatin kasar ta kara kaimi a rawar da ta ke takawa a Libya idan har tana son shirinsu a kasar ya yi nasara.