Tsohon Shugaba Mubarak na jin jiki

Hosni Mubarak Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaba Mubarak ya shafe shekaru talatin yana mulkar Masar

Kafafen yada labarai na gwamnatin Masar sun ce tsohon shugaban kasa Hosni Mubarak na nan rai a hannun Allah bayanda aka kwantar da shi a wani asibiti.

Mai shigar da kara na gwamnatin Masar ya ba da umarnin tsare Mr. Mubarak tsawon kwanaki goma sha biyar domin bincikarsa dangane da zargin karbar almundahana da cin amanar al'umma.

Yanzu haka dai ya na kwance a asibiti bayan da ciwo ya rafkeshi yayin da ake yi masa tambayoyi.

'ya'yansa biyu kuwa da su ma ake tsare da su na tsawon kwanaki sha biyar, na tsare ne a wani gidan kurkuku da ke wajen birnin al-Qahira.

Gidan talabijin na kasar ya ce an basu kayan fursuna sannan kuma ragowar 'yan jarun din sun yi ta yi mu su ihu da shewa.

Watanni biyu da su ka wuce ne dai Mr. Mubarak ya bar mulkin Masar sakamakon boren da 'yan kasar su ka yi ma sa.

Wasu daga cikinsu kuma sun fara baiyana ra'ayoyinsu game da binciken.

[