Hira ta musaman da yan takarar shugaban kasar Najeriya

Image caption Tutar Nigeria

Sashin Hausa na BBC ya yi hira da 'yan takarar shugaban kasar Najeriya da za'a gudanar a ranar asabar mai zuwa.

Manyan jam'iyyun da ke cikin takarar shugabancin kasar sun hada da PDP mai mulki, da CPC, da ACN, da kuma ANPP.

A madadin dan takarar shugaban kasa na jamiyyar ta PDP wato Dr Goodluck Jonathan, mataimakinsa, Arc Namadi Sambo ya shaidawa BBC cewa babu jam'iyyar da ta fi PDP.

A cewarsa a cikin watannin goma da suka gabata jami'yyar PDPn ta gudanar da ayyukan da suka inganta rayuwar jama'ar kasar.

Shi kuwa dan takarar shugaban kasar Najeriyar, karkashin inuwar jami'yyar adawa ta CPC , janarar Muhammadu Buhari me retiya ya ce ya kamata duk jama'a su yi wa kansu wasu tambayoyi kafin su kada kuri'ar su a ranar asabar.

Ya ce jama'a su tambayi kansu a wani mataki kasar ta ke a lokacin da jami'yyar PDPn ta karbi jagorancin kasar shekaru goma sha biyu da suka wuce kuma a wani mataki kasar ta ke a yanzu.

A dayan bangaren kuma dan takarar jam'iyyar adawa ta ACN, Malam Nuhu Ribadu cewa ya yi ya kamata 'yan Najeriya su fahimci cewa lokacin canji ya yi.

Sai dai BBC ta yi kokarin yin hira da dan takarar jami'yyar adawa ta ANPP, Malam Ibrahim Sheharau, sai dai hakar ta bata cimma ruwa ba saboda dan takarar ya bada tabbacin cewa zai tuntube BBCn idan ya shirya amma har ya zuwa daren jiya bata ji komai ba.