An kafa hukumar sasanta al'ummar Cote d'Ivoire

Shugaba Alassane Ouattara Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Alassane Ouattara

Shugaban Cote d'Ivoire, Alassane Ouattara, ya ba da sanarwar kafa hukumar tantance gaskiya da kuma sulhunta al'umma, domin binciken wadanda ke da ruwa da tsaki a rikicin da kasar ta fuskanta a baya bayan nan.

Ya na magana a bainar jama'a ne, a karo na farko tun bayan da aka kama tsohon shugaban kasar, Laurent Gbagbo, a ranar Litinin.

Mr. Ouattara ya ce yanzu ana tsare da Mr. Gbagbon a wani kebabben wuri a cikin kasar ta Cote d'Ivoire.

Shugaban Faransa, Nicolas Sarkozy, ya kare rawar da dakarun kasarsa su ka taka wurin hambarar da shugaba Laurent Gbagbo.

Ya ce, gudunmawa su ka bayar don tabbatar da mulkin demokradiyya da zaman lafiya.