Ba ni na hana kawancen CPC da ACN ba - Buhari

Jam'iyyar CPC
Image caption Jam'iyyar ACN ta zargi CPC da kawo tsaiko ga kawancen

A Najeriya dan takarar shugabancin kasar na jam'iyyar CPC, Janar Muhammadu Buhari, ya ce ba shi ne ya kawo tsaiko kan kawancen CPC da ACN ba, wanda ya tarwatse.

Ita dai jam'iyyar ACN ta zargi jam'iyyar ta CPC da kin amincewa da yarjejeniyar da suka kulla inda ya kamata a bar ma ta mukamin mataimakin shugaban kasar.

Amma Janar Buhari ya ce, abin da jam'iyyar ta ACN ta nema ya sabawa doka - domin kamata ya yi su bari a kafa gwamnati sannan a yi maganar mukaman da za a raba.

Ya kara da cewa a dokar Hukumar zabe lokacin sauya dan takara ya riga ya wuce.

'hakan bai samu ba sai karfe hudu'

Janar Buhari ya kuma ce batun da ake na cewa sun ki bayar da takardar yarjejeniya ba gaskiya ba ne, domin ACN ce ta ki amince wa da takardar bayan da farko sun nemi a kai.

Sai dai ya amince cewa ba a kai takardar a kan lokaci ba kamar yadda aka yi alkawari tun farko.

"Mun yi alkawarin kai takarda da karfe goma, amma hakan bai samu ba sai karfe hudu, kuma bayan mun kai, sai kawai muka ji sun shaida wa manema labarai cewa na hana yarjejeniya."

"Ni da nake neman shugabancin kasa, ai ko me aka ce na bayar to zan bayar domin na kai ga gaci".

Janar Buhari ya kuma bayyana dalilansa na zubar da hawaye, a yayin da yake jawabi ga magoya bayansa, a lokacin da ya ke kammala yakin neman zabensa a Abuja.

Yana mai cewa ya yi hakan ne domin tausayin halin kuncin da jama'a suke ciki a Najeriya.