Ana neman wani mutum da ya kashe mutane goma a china

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jamian yansanda a kasar China

Mutumin da ake zargi Zhou Yuxin me shekaru talatin da uku ya tsere.

Ana dai zarginsa ne da kashe mutane goma a kwanaki biyu da suka wuce a yankin Liaoning.

Cikin mutanen da ya kashe sun hada da matarsa , dansa da kuma mahaifinsa.

Mutumin dai ya malaki wani kamfanin da ake wanka da kuma wanke motocci.

Sai dai kuma an gano gawarwakin ma'aikatan dake yi masa aiki a wuraren.

Ya kuma kaiwa iyalan mai gidan da yake zama hari, inda ya halaka mutane uku.

Yan sanda, sun yi imanin cewa bin maza da yake zargin matarsa da yi ne, dalilinda ya haddasa kashe kashen.