An kashe wani dan kasar Italiya a Gaza

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu mayakan kungiyar Hamas

Ma'aikatar cikin gida ta kungiyar Hamas a zirin Gaza ta ce an gano gawar Mr Vittorio Arrigoni ne da sanyin safiya yau.

Ta ce yansanda sun samu bayanai dangane da wurin da ake garkuwa da shi amma a lokacin da iso wurin sun tarar da Mr Arrigoni a rataye.

Sun kuma ce ya mutu ne fiye da wasu awowi da suka wuce.

Dan kasar italiyar me fafutukar kwato yancin Falasdinawa ya shafe shekaru da dama yana zama a Gaza.

Da safiyar jiya alhamis ne mayakan wata karamar kungiyar islama a Gaza da ake kira Salafists suka sace shi.

Kungiyar bata ga maciji da Hamas wadda takewa kallon kungiya me sassaucin ra'ayi.

Ta kuma bukaci Hamas ta sako mata wasu membobinta dake tsare a wani gidan yari , inda ta debar mata wa'adin yammaci yau.

Mr Arrigoni dai shine dan kasan waje na farko da za'a sace a zirin Gaza tun bayan shekerar 2007 da aka sace Alan Johnston wani dan jarida me aiki da BBC .