Nato na neman tallafin kasashenta

Taron NATO a Jamus Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Burtaniya da Faransa na cigaba da kokarin shawo kan sauran kasashen da ke cikin kawancen NATO da ke taro a Berlin da su shiga a dama da su a cikin hare-haren da ake kaiwa kasar Libya.

Sakatariyar hulda da kasashen waje ta Amurka, Hillary Clinton ta shaidawa sauran ministocin cewa ya zama wajibi kawancen NATO su kafe kan kudirinsu na yaki da kanar Gaddafi.

Spain ta ce a shirye ta ke ta cigaba da ba da gudunmawa amma dai ba za ta shiga cikin kasashe masu kai hari ba.

Sakatare janar na NATO, Anders Rasmussen ya jaddada cewa manufar kawancen ita ce kare al'ummar Libya.