An gurfanar da mutane goma sha shidda a gaban kotu a jahar Kano

Image caption Jamian yansanda Najeriya

Rundunar yan sandan a jahar Kano ta ce ta gurfanar da mutane goma sha shida a gaban kotu inda take zarginsu da aikata laifuka daban daban a lokacin zabukan da suka gabata a ranar asabar din da ta gabata.

Ta ce tana zarginsu ne da aikata laifukanda suka sabawa dokokin zabe, wadanda suka hada da yunkurin tada hankula.

Kakakin rundunar yan sandan ta jahar Kano ASP Magaji Musa Majiya ya ce an kuma wasu da suka malaki makamai irinsu aduna da kuma kwayar wiwi.

Sai dai ya ce wanan alama ce dake nuni da cewa jama'a sun yi biyaya da kirayen kirayen da rundunar yan sanda ta rika yi akan bukatar ganin cewa an bi doka da oda, saboda adadin mutanen da aka kama ba shi da yawa sosai.