Babu zaben gwamnoni a jihohi biyar a Najeriya

Image caption Shugaban hukumar zaben Najeriya, Farfesa Attahiru Jega

Kotun daukaka kara dake birnin tarayya Abuja ta yanke hukuncin cewa ba za'a gudanar da zaben gwamnoni wanda za'a yi ranar 26 ga watan Aprilu a jihohi biyar ba.

Jihohin dai sun hada da Adaamwa, da Bayelsa, da Cross Rivers, da Kogi, da kuma Sokoto. Kotun dai ta bayyana cewa gwamnonin Jihohin wanda hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta daukaka kararsu gare ta, za su karasa wa'adin mulkinsu.

In da ta bayyana cewa gyaran fuskar da aka yiwa kundin tsarin mulki na shekarar 1999 wanda ya tanadi cewa duk wani gwamna da aka rushe zabensa, wanda za'a nada a gaba, zai cika wa'adin mulkin ne ba sabon wa'adi ba.

Don haka kotun ta ce wannan ba zai shafi gwamnonin ba, tunda lokacin da aka rantsar da su ba'a yiwa kundin tsarin mulki gyaran fuska ba.

A zaman kotun na yau karkashin jagorancin mai sharia Mohd Lawal Garba, kotun daukaka karar ta yanke hukuncin cewa ba za'a yi zaben gwamnoni a Jihohin Adamawa da Bayelsa, da Cross Rivers, da Kogi, da kuma Sokoto ba.

Kwaskwarimar tsarin mulki

Kotun ta yanke hukuncin cewa lokacin da aka rantsar da gwamnonin ba a riga an yiwa kundin tsarin mulki na shekarar 1999 kwaskwarimar ba.

Paul Irokoro daya daga cikin Lawyan gwamnonin ya yi karin bayani akan hukuncin kotun.

"Ya kamata mutane su fahimci cewa matsayin kotu shine fassara doka kamar yanda ta ke, ba wai yanda mutane ke so ta kasance ba.

"Kundin tsarin mulkin dai a bayyane yake. Kana da shekaru hudu daga ranar da aka rantsar da kai, sannan kuma idan ma aka rantsar da kai bayan an yi zagaye na biyu na zabe, shekaru hudun za su fara ne daga lokacin da aka rantsar da kai din. Sam babu wani dalili na samun rashin jituwa.

"Bamu san ma dalilin da ya sa har aka kawo wannan batun gaban kotu ba. Da kuma dalilan da suka sa INEC ke tunanin yin zabe a wadannan jihohin bayan dokar a bayyane take." In ji Paul Irokoro.

To sai dai Lawyan INEC Hassan Liman ya ce za su shawarci hukumar zabe domin ganin ko shin zasu daukaka kara zuwa kotun koli, ko kuwa zasu amince da wannan hukuncin:

"A koda yaushe muna cewa kundin tsarin mulki ne ya kirkiro hukumar INEC. Wannan hukunci ne da kotun da ke da hurumin saurarar karar ta bayar.

"Kuma kamar yanda hukuncin yake a yau shine hukumar INEC ba za ta gudanar da zabe a wadannan jihohin ba, kamar dai yadda yake a hukuncin yau din.

Amma idan muka shawarci hukumar ta kuma tabbatar da cewa akwai bukatar daukaka kara, to wannan na nufin cewa akwai sauran rina a kaba, wato sauraron sakamakon karshe daga bakin kotun koli wato Supreme Court." In ji Hassan Liman.

Wannan hukuncin wanda ke nufin cewa ba za'a yi zaben gwamnoni ranar 26 ga watan Aprilu a Jihohi biyar din ba, ya biyo bayan daukaka kara da hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta yi akan Jihohin biyar wadanda suka hada da Adamawa, da Bayelsa, da Cross Rivers, da Kogi, da kuma Sokoto, inda take kalubalantar matakin babbar kotun tarayya akan fassara bangaren dokar da ya bada damar cewa gwamnonin jihohin za su cika wa'adin mulkinsu na shekaru hudu tun da lokacin da aka rantsar da su ba'a riga an yiwa doka gyaran fuska ba.