Fararen hula da dama sun mutu a Misrata

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Likitoci na duba wadanda suka jikkata a Misrata

Wani wakilin BBC da ya samu shiga birnin Misrata dake yammacin Libya ya ce ana ci gaba da kai mutanen da suka jikkata asibitoci a yayinda fararen hula da dama su ka mutu.

Ana dai ci gaba da fafatawa ne tsakanin 'yan tawaye da kuma dakarun da ke biyayya ga Kanal Gaddafi kusan makwanni bakwai kenan da su ka gabata a birnin.

Likitocin dake asibitin sun shaidawa Wakilin BBC cewa mutanen da ake kawowa asibiti fararen hula ne da su ka samu rauni sanadiyar harbe-harben bindigogi da kuma bamai-bamai.

Kusan dai kashi tamanin na mutanen da suka mutu a birnin fararen hula ne kuma wakilin BBC dake birnin ya ce ana shigowa ne da agaji birnin ta tashar jirgin ruwa.