Amurka zata taimakawa kamfanin Fukushima

Kamfanin dake kula da cibiyar makamashin nukiliya ta Fukushima ya ce zai kai nan da karshen shekara kafin ya kammala shawo kan matsalar da cibiyar ke fama da ita.

Kamfanin na Tepco ya ce zai dauke shi nan da watanni uku masu zuwa, ya yi kokarin rage yawan tururin nukiliyar dake fita daga cibiyar makamashin nukiliya ta Fukushima.

Wannan jawabin ya biyo bayan ziyarar Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton wadda ta yi musu tayin goyon baya daga Amurka.

Wakiliyar BBC tace Akwai matukar damuwa da tausayawa da kuma sha'awa kan irin juriya da kwazon da al'ummar Japan suka nuna a daidai wannan lokaci da suke cikin wahala.