Sakamakon zaben Shugaban kasar Najeriya

Image caption 'Yan takaran da su ke kan gaba a zaben sune, Shugaba Goodluck Jonathan na PDP da kuman Janar Muhammadu Buhari na CPC.

20:09 Mun kawo karshen bayanai da muke kawo muku a wannan shafin. Sai ku kasance da mu a shirye-shiryen mu na rediyo domin samu karin bayani.

19:36 Wakilin BBC Nura Muhammed Ringim: Hukumar zaben jihar Kaduna ta bayyana jam'iyyar CPC, a matsayin wadda ta lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar jiya, yayin da jam'iyyar PDP ke bi mata.

19:32 Wakilin BBC Abba Mohammed Katsina: A jihar Katsina jami'yyar CPC ta koka akan cewa, hukumar zaben INEC reshen jahar ta zaftare yawan kuri'un da ta samu.

18:40 Wakiliyar BBC, Bilkisu Babangida: A jihar Yobe rahotanni sun nuna cewar Jam'iyar CPC ce ke kan gaba a sakamakon da aka bayyanawa manema labaran da yammacin yau.

18:20 Sakamakon zaben shugaban kasa na jihar Nasarawa: ACN 1,204 ANPP 1,047 CPC 278,390 PDP 408,997

18:20 Sakamakon zaben shugaban kasa na jihar Oyo: ACN 252,240 ANPP 7,156 CPC 92,396 PDP 484,758

18:13 Sakamakon zaben shugaban kasa na jihar Ekiti: ACN 116,981 ANPP 1,482 CPC 2,689 PDP 135,009

18:08 Sakamakon zaben shugaban kasa na jihar Imo: ACN 14,821 ANPP 2,520 CPC 7,591 PDP 1,381,357

17:36 Zaben 2011 na zubar da hawaye sosai a kan kasa ta Najeriya ganin irin yadda a wani bangare kasata sabo da bambancin addini da kabilanci mutane suka zabi cig aba da zama cikin wahala da kangin rayuwa, a wani bangaren Najeriya wasu saboda jahilci da mutuwar zuciya suka zabi dawwama cikin talauci da musifa saboda dan kudi kadan suka saida kuri'unsu. Ina ma ace ina da wata kasa inda kabilanci da kudi basa da tasiri wajen neman yanci in koma can in huta da bakin ciki. Daga Umar Gardi a Sokoto.

17:28 Sakamakon zaben shugaban kasa na jihar Sokoto ACN 20,144 ANPP 5,063 CPC 540,769 PDP 309,057

17:22 Sakamakon zaben shugaban kasa na jihar Lagas ACN 427,203 ANPP 8,941 CPC 189,983 PDP 1,281,688

17:09 Sakamakon zaben shugaban kasa na jihar Anambra ACN3,437 ANPP 975 CPC 4,223 PDP 1,145,169

16:51 Yusuf Ibbi BBC Hausa Facebook: Yakamata a rusa zabe inda akayi magudi, in har anason ace anyi zabe mai inganci.

16:46 Wakilin BBC a Bauchi, Ishaq Khalid: Hankali ya fara kwantawa a jihar Gombe, bayan zanga zangar da aka gudanar yau a jihar, saboda zargin an tafka magudi a zaben shugaban kasar da aka yi a jihar jiya.

16:00 Abubakar Dahiru BBC Hausa Facebook: Mun san yanzu lokacin siyasa ne, kuma kowa yanada 'yancin shiga ko wace jam'iyya to amma wannan zaben wata adawa ce tsakanin kudancin da arewacin Najeriya.

15:50 Najeriya anyi zabe angama lafiya, saura sakamako, a gaskiya Jega kacancanci yabo, domin kaine mutum na farko da ka fara kamanta gaskiya da adalci a hukumar zabe. To Allah yayi mana jagora amin. Daga Lawal Abba, karamar hukumar Batsari a jihar Katsina state.

15:41 Wakiliyar BBC a Maiduguri, Bilkisu Babangida: A jihar Borno sakamakon zaben shugaban kasar ya nuna cewar Jam'iyar CPC ita ke da rinjaye da kimanin kuri'u dubu dari tara da tara da dari bakawai da sittin da uku,yayinda Jam'iyar PDP ke biye da ita da Kuri'u dudu dari biyu da bakawi da saba'in da biyar.

15:35 Sakamakon zaben shugaban kasa na jihar Osun: ACN 299,711 ANPP 3,617 CPC 6,997 PDP 188,409

15:30 Sakamakon zaben shugaban kasa na jihar Ondo: ACN 74,253 ANPP 6,741 CPC 11,890 PDP 387,376

15:11 Wakilin BBC a Lagas, Umar Shehu Elleman: A jihar Lagas jam'iyyar PDP ta samu galaba kan jam'iyyun ACN da CPC, wanda tuni aka aike da sakamakon zuwa shelkwatar hukamar zaben kasar dake Abuja.

15:07 Wakilin BBC a Katsina Abba Mohammed Katsina: A Katsina, yayin da ake bayyana sakamakon zaben shugaban Najeriyar na jiya, rahotanni sun ce wani mutum daya ya rasa ransa, kuma wasu biyu suna can kwance asibiti rai hannun Allah, sakamakon harbin da wani jami'in tsaro yayi da cikin garin Katsinar.

14:38 Nas Muhammad BBC Hausa Facebook: Aboki na a Akwa Ibom ya ce mun a mazabar su ba'a yi zabe ba. Wai sun jira ba wani jami'in zabe. Sai can wajen karfe biyar na yamma sai ga wani ya kawo masu dubu dari biyar.

14:30 Farfesa Jega kayi amfani da gaskiya wajen bayyana saka makon zabe, in hakan zai samar da zaman lafiya a Nigeria. Daga Lawal Sani Nakawu Daura.

14:23 Sadiq Ahmed BBC Hausa Facebook: Manyan arewa ku ke cutar arewa. Allah shine kawai gatan talakawa.

14:02 Wakilin BBC Muhammed Annur Muhammed: A jihar Jigawa dake arewacin Najeriya sakamakon zaben shugaban kasar da akayi jiya ya tsayane a tsakanin jam'iyar adawa ta CPC wadda ta sami nasara a kananan hukumomi 23 daga cikin 27 na jihar yayinda jam'iyyar PDP mai mulki ta yi galaba a sauran kananan hukumomin.

13:59 Jega jega duniya na kallanka, kuma al'ummar Najeriya na kallanka,kamana adalci ga sakamakon zabe, jiya munsha rana ,tun safe har yanma. Daga Aisha matar Muhd Ahmad a Kabuga Kano.

13:50 Jama'ar Najeriya, da Jami'an Zabe, ina kira gareku da kuyi adalci ku fitar da sakamakon wannan zabe. Jami'an tsaro na kasa su kula da duk wani tashin hankali da zai auku saboda sakamakon. Victor daga Yauri.

13:42 Sakamakon zaben shugaban kasa a jihar Enugu: ACN 1,755 ANPP 1,111 CPC 3,753 PDP 802,144

13:38 Sakamakon zaben babban birnin tarraya Abuja: ACN 2,327 ANPP 3,170 CPC 131,576 PDP 253,444

13:32 Sakamakon zaben shugaban kasar jihar Ogun: ACN 199,555 ANPP 2,969 CPC 17,654 PDP 309, 177.

13:12 Muna matukar murna da zaben da ya gabata jiya a Najeriya. Allah ya taimake mu amin. Yakamata 'yan siyasa su daina magudi. Daga kabir sani gwarzo. Kano, Najeriya.

13.00: Sade Saidu Daura BBC Hausa Facebook: Tashe tashen hankula da kone kone ba shi zai kawo mana ci gaba ba. Fadar sakamako na gaskiya shine zai kwantar da hankalin jama'ar Najeriya.

12:58 A yanzu haka dai an fara samu sakamakon zabe a sassan Najeriya. A yanzu haka dai INEC ta ce ta samu sakamakon jihohi biyar, kuma nan ba da dadewa ba za'a bayyana su.