Kidayar kuri'un zaben shugaban kasa a Najeriya

Hakkin mallakar hoto Reuters

A Najeriya ana cigaba da kidayar kuri'u, bayan zaben shugaban kasar da aka yi jiya Asabar.

Alamun farko na nuna cewa, ana gogayya sosai tsakanin shugaban kasar mai ci a yanzu, Goodluck Jonathan, da kuma tsohon shugaban mulkin sojan kasar, Janar Muhammadu Buhari mai ritaya.

Jam`iyyun siyasa ashirin ne suka shiga takarar.

'Yan kasashen wajen da suka kula da yadda aka kada kuri'ar, sun ce mai yiwuwa zaben ya kasance shine mafi sahihanci a kasar, a cikin shekaru da dama.