Ana matukar bukatar agaji a Misrata

Babbar jami'ar MDD mai kula da ayyukan ji kai, Valery Amos ta yi kiran a tsagaita bude wuta a Libya don bada damar kiyasta yawan agajin da fararen hula ke bukata.

Yayinda take jawabi a birnin Benghazi, wanda ke karkashin ikon 'yan tawaye, Baroness Amos ta ce gwamnatin Libya ta ba ta tabbacin cewa zaa kyale ma'aikatan agaji na MDD su gudanar da ayyukansu a cikin kasar ta Libya.

Baroness Amos ta kara da cewa dubban jamaa na bukatar magunguna matuka a birnin Misrata, wanda sojojin gwamnatin Libyar ke cigaba da yi wa ruwan bama-bamai.

Birtaniya ta ce za ta dauki nauyi aikin kwashe fararen hula masu yawa daga birnin Misrata ta jiragen ruwa.