Ana zanga zanga a arewacin Najeriya

Masu zanga zanga a Najeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu zanga zanga a Najeriya

Rikici ya barke a wasu jahohin arewacin Najeriya, bayan da alamu ke nuna cewa shugaban kasar mai ci, Goodluck Jonathan ya yi nasara a zaben shugaban kasar da aka yi ranar Asabar da ta gabata.

Bayan an kidaya kusan duka kuru'un da aka kada, yawan kuru'un da Mr Jonathan ya samu sun kusan ribanya har sau biyu na babban abokin takararsa, Janar Mohammadu Buhari.

Masu zanga zanga a jahohi kamar Kaduna, Kano, Borno, Sokoto, Bauchi da dai sauransu na nuna rashin jin dadinsu game da sakamakon zaben shugaban kasar da suka ce an tabka magudi.

Masu zanga zangar na ta kone kone a kan tituna da kuma kai hari kan manyan jami'an jam'iyyar PDP da ma wasu shugabannin al'umma.

Nan gaba a yau ne ake sa ran Hukumar zaben kasar, INEC za ta bayyana duka sakamakon zaben.